Saddeq(guest
2017-12-13 12:36
An kama wata mata 'yar Najeriya bisa zargin sayar da tagwayen jariranta 'yan wata guda.
Lamarin ya faru ne a jihar Katsina da ke arewacin kasar.
Ana tuhumarta ne da laifin safarar yara, amma 'yan sanda sun ce za a iya kara tuhumarta da wasu laifukan na daban.
Rahotanni sun ce matar ta yi yunkurin sayar da 'ya'yan nata mata tagwaye a kan naira 350,000 ga wani mutum, wanda shi ne ya gaya wa 'yan sanda.
Matsalolin sayar da jarirai da safarar yara sun jima a Najeriya.
Matar, 'yar shekara 30, ba ta yi wani bayani ba da aka gurfanar da ita a gaban kotu a birnin Katsina, amma wani shafin intanet na Gistmania ya bayyana cewa ta ce aikin shaidan ne.
*. Nigeria: An dakatar da wani Basarake saboda 'fyade'
*. Nigeria ta ce ta duƙufa don kafa matatar mai a Katsina
Hukumar hana safarar mutane a Najeriya (NAPTIP) ta bayyana cewa binciken da ta gudanar a shekarar 2011 ya nuna cewa a kan sayar da jarirai a kan $6,400.
A shekarar 2013, 'yan mata 17 masu juna biyu da jarirai 11 aka kubuto daga wani gida da ake haifar jarirai domin a sayar da su a jihar Imo.
Duk da nuna tsananin rashin jin dadi da jama'a su ka yi da kuma alkawarin gwamnati na cewa za ta dauki manyan matakai domin magance matsalar, iyaye mata a Najeriya sun ci gaba da siyar da 'ya'yansu.
Shekara biyu bayan an bankado gidan haihuwar jariran a Imo, an kama wata mata yayin da ta ke kokarin siyar da jaririnta a kan dala 90 ko kuma fan 67 a Jihar Cross River a kudu maso gabashin Najeriya.